Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kolin Zaman Lafiya a Kwango - 2003-04-11


Kasar Uganda ta yarda ta janye sojojinta daga kasar Congo Kinshasa domin a rage zaman zulumi kana kuma ta nuna goyon bayan ta ga gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Kwango.

Shugaba Yuweri Museveni ya ce sojojinsa zasu fice daga kasar ta Congo kafin ranar 24 ga wannan Wata na Afirilu.

Ya bayar da wannan sanarwa ne a yayin taron da aka yi a ranar Laraba na wasu shugabannin kasashen Afirka 5 a birnin Capetown na kasar Afirka ta Kudu. Bayan taron ne shugaban kasar Congo, Joseph Kabila ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya data gudanar da bincike game da kisan Kare Dangin da aka yi a cikin makon jiya wanda aka halaka kimanin fararen hula dubu daya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Duk da yadda aka fara aiki da wani shirin zaman lafiyar da zai kawo karshen yakin basasar kusan shekaru 5 a kasar ta Congo, har yanzu an ci gaba da fama da tarzoma a tsakanin kungiyoyin tawayen yankunan kasar da kuma kungiyoyin kabilun dake arewa maso gabashin kasar, inda Uganda ta girke sojojin ta bisa bukatar Majalisar Dinkin Duniya domin su taimaka a samu zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG