Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Zaben Nigeriya - 2003-04-24


Jam’iyyun adawar Nigeriya sun buƙaci sai lallai azimin, shugaba Olusegun Obasanjo ya yi murabus daga kan mukaminsa, kana kuma a gudanar da sabon zaben shugaban kasar, suna masu cewa babu wata tantama cewa an tufka kazamin magudi a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar asabar data gabata.

A shekaran-jiya (Talata) ne hukumar zaben Nigeriya ta aiyana cewa Obasanjo ne ya lashe zaben da kashi 62 cikin 100 na kuri’un da aka kada, inda ya kayar da babban mai adawa da shi, Mohammadu Buhari, wanda ya samu kashi 32 cikin 100 kacal na yawan kuri’un da aka kada a zaben.

To amma kuma wata Gamaiyar jam’iyyun adawa guda 29 na Nigeriya, ta yi barazanar daukar wani matakin bijirewar da bata baiyana fasalinsa ba, muddin shugaban ya yi kunnen-uwar-shegu da wannan bukata ta yin murabus a ranar 29 ga watan Mayu. Bugu-da-kari, hadakar jam’iyyun adawar sun ce zasu gurfana a Mashari’anta (Kotu) su bukaci sai lallai azimin a gudanar da sabon zabe.

To amma shugaba Obasanjo ya sa kafa ya yi fatali da wannan korafi. Shugaban ya yi kashedi tare da jan kunne da yin barazanar murkushe duk wata zanga-zangar da talakawan kasar zasu yi dangane da wannan zabe. A jiya (Laraba), shugaban jam’iyyar PDP Audu Ogbe ya shedawa manema labarai cewa gwamnatinsu ba ta yarda a gudanar da wata zanga-zanga ba. Ya ce, nuna bijirewa ya sabawa tsarin mulki kuma haramun ne kuma wani abin assha ne, kuma zasu yi amfani da karfi mai tsanani su murkushe duk wata zanga-zanga a kasar.

A cikin makon jiya ne Buhari, wanda aka ce an kayar a zaben shugabancin kasar ta Nigeriya ya yi barazanar cewa zai bukaci talakawa su bijirewa sakamakon zaben shugaban kasar, wanda ‘yan adawar duk suka yi iktifatin cewa an tufka magudinsa. To amma yanzu, Buhari ya nuna alamun janye jikinsa daga wannan barazana da ya yi da kuma shawarar kalubalantar sakamakon zaben. Wasu kungiyoyin ‘yan kallon zaben na gida da waje, sun ce babu tantama ko tababa cewa hakika an tufka kazamin magudi da zarmen kuri’u da munakisa da almundahana a wasu jihohin kasar ta Nigeriya a lokacin zaben na ranar Asabar. Gwamnatin Amurka ta bukaci sai lallai gwamnatin Nigeriya ta saurari tare da warware wannan zargi na aikata magudi a zabubbukan kasar.

XS
SM
MD
LG