Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin aikin kasar Zimbabwe ya shiga rana ta biyu - 2003-04-24


Ana sa ran za a ci gaba da gagarumin yajin aikin sai-baba-ta-gani na kwanaki ukku da ake yi a Zimbabwe domin nuna adawa da gagarumin karin farashin Man fetur da gwamnati ta yi, inda za a shiga rana ta biyu ta wannan yajin-aiki a yau alhamis.

A jiya laraba aka fara wannan yajin aiki, inda aka rufe akasarin kantuna da opisoshin gwamnati a manyan alkaryun kasar. Ba a bayar da rahoton wata tarzoma ko hatsaniya ba a lokacin da aka gudanar da irin wannan yajin aiki a cikin watan jiya.

Gwamnatin kasar ta yi tur da wannan yajin-aiki, tana mai cewa wani yunkuri ne da kungiyoyin adawa suke yi su sabatta tattalin arzikin kasar tare da kawar da gwamnatin shugaba Robert Mugabe daga mulkii da karfin tsiya. An haramta yin yajin-aiki a kasar. To amma kuma babbar gamaiyar kungiyoyin kwadagon kasar ta Zimbabwe, wacce take adawa da karin farashin Man na makon jiya, ta ce duk da wannan haramci za a ci gaba da wannan yajin aiki.

XS
SM
MD
LG