Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta ce a Shirye take ta kulla zaman lafiya da Palasdinawa - 2003-04-24


Praiminista Ariel Sharon na kasar bani Isra’ila ya ce gwamnatinshi zata yi bakin karfinta wajen kulla wata yarjejeniyar siyasar sasantawa wacce zata samar da zaman lafiya tsakaninsu da Palasdinawa.

Mr. Sharon yana mayar da martani ne ga labaran da aka bayar cewa shugaban Palasdinawa Yasser Arafat da prime ministan palasdinawa mai jiran gado mai sassaucin ra’ayi, Mahmoud Abbas sun cimma daidaituwa a jiya laraba game da sabuwar gwamnatin Palasdinawan.

Mr. Sharon ya shedawa gidan Radiyon Isra’ila cewa dukkanin Yahudawa suna kaunar zaman lafiya, to amma ya ce abu ne mai muhimmanci su ma bangaren Palasdinawa su nuna bukatar cimma zaman lafiya.

Malam Arafat ya tsaya kai-da-fata yana adawa da sabon ministan tsaron da Mr. Abbas ya zaba. An yi makonni biyu ana fama da wannan taƙaddama wacce ta yi barazana ga daukacin shirin sulhun yankin na Gabas Ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG