Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi wa Farisa Gargadi Game Da kasar Iraq - 2003-04-24


Gwamnatin shugaba Bush ta ce ta fito fili balo-balo ta yi kashedi ga gwamnatin Iran da kada ta kuskura ta tsoma hannu ko baki da nufin sanya cikas ga turbar da Iraqi ta kama na kafa tsarin tsarin demokaradiyya a kasar.

A jiya laraba ne fadar White House ta mayar da martani ga wani labari da jaridar New York Times ta buga cewa jami’an gwamnatin Iran sun tsallaka sun shiga yankin kudancin kasar Iraq domin kulla dangantakar abota da Maluman Musulmin Shi’a kana kuma su yayata bukatun kasar ta Iran a yankin.

Wani kakakin Fadar ta White House bai tabbatar da gaskiyar labarin jaridar ba. To amma ya ce duk wani yunkuri da wata kasa ko wani mahaluki zai yi daga wajen kasar ta Iraqi domin ya haifar da abin da aka yi amanna abun alheri ne ga jama’ar ta kasar ta Iraqi, ba zai samu nasara ba. A Halin da ake ciki kuma, sojojin Amurka sun kara damke wasu manyan jami’ai ukku na gwamnatin tsohon shugaba Saddam Hussien a jiya laraba, wadanda suka hada da mutum na goma a jerin mutanen da Amurka ta fi nema ruwa-a-jallo a kasar ta Iraqi.

Babbar cibiyar gudanar da harkokin yakin Amurka a kasar ta Iraqi ta ce sojojin na Amurka sun damke tsohon babban kwamandan aiyukan tsaron kasar Iraqin, Muzahim Sa’b Hassan al-Tikriti, wanda shine mutum na 10 a jerin mutane 55 da Amurka take nema afujajan a cikin kasar ta Iraqi.

Shi, dangin Saddam Hussien ne kana kuma an ce ya taimaka ainun wajen horas da zaratan mayakan sa kan nan na Fadayeen masu cikakkiyar biyayya ga shugaba Hussien.

Haka kuma sojojin na Amurka sun kame tsohon ministan cinikin kasar ta Iraqi, wanda shine mutum na 48 a cikin wancen jerin mutane, yayin da aka a jiyan (laraba), tsohon kwamandan rundunar leken asirin sojin Iraqin ya mika kansa ga sojojin na Amurka. Shine mutum na 21 a jerin mutanen da Amurka take farauta a kasar.

An kashe ko kuma sojojin taron dangi sun kame 14 daga cikin mutanen da Amurka take nema ruwa-a-jallo a kasar ta Iraqi.

XS
SM
MD
LG