Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Mazhabin Shi'a Sun Yi Maci A Iraqi... - 2003-05-19


Dubban Musulmi 'yan mazhabin Shi'a na kasar Iraqi sun yi maci a birnin Bagadaza, suna kiran da a kafa gwamnatin rikon kwarya ta 'yan Iraqi, a kuma janye sojojin Amurka daga kasar.

Kafofin labarai na kasashen yammaci sun ce mutanen da yawansu ya kai dubu 10 dake rera waka suna dauke da kwalayen da aka rubuta kalamun nuna kyamar Amurka, sun yi maci yau litinin a babban birnin kasar zuwa daya daga cikin wuraren ibada mafiya tsarki na 'yan Shi'a.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta MDD yayi kashedin cewa ana iya fuskantar bala'in nukiliya a kasar Iraqi.

A cikin sanarwar da ya bayar a birnin Vienna, Mohammed el-Baradei ya ce ya damu sosai da rahotannin kwasar ganima da lalata kayayyaki a cibiyoyin nukiliya na Iraqi. Ya roki Amurka da ta kyale kwararrun hukumar su koma Iraqi.

XS
SM
MD
LG