Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Suna Shirin Yin Gwajin Wani Maganin Rigakafin Cutar Kanjamau - 2003-05-19


Kwararrun dake kokarin yaki da cutar kanjamau ta AIDS ko SIDA a kasar Botswana, sun ce suna shirin yin gwahjin wata sabuwar alllurar rigakafi su ga ko ba zata yi lahani ga bil Adama ba.

Wannan kungiyar kwararru zata yi gwajin sabuwar allurar rigakafin da mutane 42 wadanda suka zabi yin haka domin radin kansu a Botswana da Amurka. Wannan zai zamo gwajin allurar rigakafin kanjamau na farko da za a yi a lokaci guda a Afirka da kuma Amurka.

Ana kiran wannan allurar rigakafin kanjamau da za a yi gwajinta EP HIV-1090, kuma wani kamfani dake San Diego a Jihar California ya kirkiro ta. Ba za a yi amfani da wata kwayar halittar HIV mai rai a wannan gwajin ba, matakin da zai kawar da yiwuwar kamuwa da wannan cuta a bangaren masu yin gwajin.

XS
SM
MD
LG