Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Ambaliyar Ruwa Ya Zarce 200 A Sri Lanka - 2003-05-20


Jami'an Sri Lanka sun ce yawan mutanen da suka mutu a mummunar ambaliyar ruwan da aka yi cikin makon nan a yankin tsakiyar kudancin kasar ya zarce 200, yayin da har yanzu akwai mutanen da yawansu ya kai kusan haka da suka bace, ake kuma fargabar cewa sun mutu.

Jami'ai suka ce mutane fiye da dubu 150 sun rasa matsuguni a sanadin ambaliyar ruwa da laka, wadanda suka biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi kwana da kwanaki ana juyewa.

An bayyana wannan lamari a zaman bala'i mafi muni da kasar ta gani cikin shekaru fiye da hamsin.

Jami'ai suka ce sun kasa auna munin lamarin sosai a saboda kungiyoyin agaji sun kasa kaiwa ga da yawa daga cikin yankunan da ambaliyar ta fi yi wa barna.

Gwamnatin Sri Lanka ta ware kudi fiye da dala dubu 60, domin agajin gaggawa.

XS
SM
MD
LG