Jami'an MDD sun ce dubban mutane suna gudu daga Liberiya zuwa kasashe makwabtanta, a bayan wani sabon farmakin da 'yan tawaye suka kaddamar a can.
Jami'an hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar sun ce a cikin kwanaki biyun da suka shige, dubban 'yan Liberiya sun arce zuwa Ivory Coast. Suka ce mutane sun fara tserewa a karshen mako, a lokacin da garin Harper dake bakin teku ya fada hannun 'yan tawayen Liberiya.
Jami'an MDD sun ce sun damu da yawan mutanen da suka rasa matsuguni a sanadin wannan fada.
Labarin wannan fada da kuma gudun hijirar da dubban mutane suke yi ya zo kwana guda a bayan da shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, Ruud Lubbers, ya kammala rangadin kasashe biyar domin nazarin matsalar 'yan gudun hijira a yankin, inda har ya ce shugaba Charles Taylor na Liberiya, shine ke haddasa babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma.