Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Sun Bukaci Da A Koma Kan Teburin Shawarwarin Neman Zaman Lafiya A Indonesiya - 2003-05-20


Kasashen duniya sun bukaci gwamnatin Indonesiya da 'yan awaren lardin Aceh da su koma kan teburin shawarwarin neman cimma zaman lafiya, a bayan da gwamnati ta kaddamar da farmakin soja a wannan lardi mai fama da fitina a arewacin kasar.

Kasashen Australiya, Japan, Amurka, Tarayyar Turai da wasunsu, sun yi kira ga sassan biyu da su kawo karshen sabon fadan da ya barke jiya litinin a bayan wargajewar taron zaman lafiyar da aka shirya a birnin Tokyo.

Amma kuma a daidai lokacin da shugabannin duniya suke rokon da a bai wa zaman lafiya damar zama da gindinta, babban hafsan sojojin gwamnatin Indonesiya, Janar Endriartono Sutarto, ya umurci dakarunsa da su murkushe dukkan 'yan tawaye daga lardin.

Babu wani rahoton da aka samu na gwabza kazamin fada a yau talata, amma kuma jami'an lardin sun ce an cinna wuta a makarantu da gidaje da ofisoshin gwamnati a sassa da dama na lardin.

Dukkan bangarorin biyu suna zargin junansu da aikata wannan ta'asa.

XS
SM
MD
LG