Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ai A Sa'udiyya Suna Zaman Tsammanin Fuskantar Hare-haren Ta'addanci - 2003-05-20


Jami'ai a Riyadh, babban birnin Sa'udiyya, suna zaman yiwuwar fuskantar karin hare-haren ta'addanci kamar na makon jiya da yayi sanadin mutuwar mutane 34.

Ofishin jakadancin Amurka dake birnin Riyadh ya ce za a rufe dukkan kananan ofisoshin jakadancin Amurka dake kasar tare da shi kansa babban ofishin jakadancin daga gobe laraba, a saboda labarin da aka samu cewar akwai harin ta'addancin da aka shirya kaiwa.

Ya ce za a ci gaba da rufe ofisoshin akalla har zuwa ranr 25 ga wata, watau lahadi.

Dandalin ofishin jakadancin na duniyar gizo, ya ce jami'ai sun samu bayani mai tushe cewar ana shirya kai karin hare-haren ta'addanci kan cibiyoyin Amurka a daular Sa'udiyya.

Hukumomin Sa'udiyya sun kara tsaurin matakan tsaron da suke dauka. Jami'an na Sa'udiyya sun ce kungiyar al-Qa'ida ce ke da alhakin hare-haren da aka kai ranar litinin din makon jiya a Riyadh, inda aka kashe Amurkawa 8.

XS
SM
MD
LG