Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Janye Sojojinta Daga Bait-ul-Hanoun - 2003-05-20


A yau talata sojojin Isra'ila sun janye daga garin Baitul Hanoun na zirin Gaza, wanda suka shiga suka mamaye a makon jiya domin hana Falasdinawa kai hare-hare da rokoki cikin Isra'ila.

Mazauna garin suka ce kafin su janye din, sai da sojojin bani Isra'ila suka rushe gidaje, suka lalata hanyoyin mota, suka tuge bishiyoyi sannan suka tsinka wayoyin tarho.

Daga nan sojojin suka koma bayan wannan gari wanda ke wani yankin bakin iyakar da Isra'ila ta ce zata mikawa dakarun tsaron Falasdinawa idan dukkan sassan suka yarda zasu aiwatar da shirin da Amurka ta gabatar na cimma zaman lafiya.

A ranar asabar an tashi daga wani taro tsakanin firayim ministan Isra'ila Ariel Sharon da takwaransa a bangaren Falasdinawa, Mahmoud Abbas, ba tare da cimma yarjejeniya kan aiwatar da shirin zaman lafiyar ba.

Isra'ila ta rufe bakin iyakokinta da zirin Gaza da kuma yankin Yammacin kogin Jordan ranar lahadi a bayan hare-haren kunar-bakin-waken da suka yi sanadin mutuwar bani Yahudu su akalla 12.

XS
SM
MD
LG