Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sasantawa Ta Ivory Coast Zata Gana A Tungar 'Yan Tawaye - 2003-05-22


An shirya wakilan gwamnatin sasantawa ta kasa ta Ivory Coast zasu gana yau alhamis a birnin Bouake dake hannun 'yan tawaye.

A can baya, wakilan gwamnatin sun gudanar da tarurrukansu ne a cibiyar kasuwanci ta kasar, Abidjan, ko kuma cibiyar mulki watau Yamoussoukro. Dukkan wadannan birane biyu suna hannun sojoji masu biyayya ga shugaba Laurent Gbagbo.

Taron da wakilan gwamnatin zasu yi yau an shirya gudanar da shi tun ranar talatar da ta shige, amma sai aka dage a saboda matsaloli na tsaro. An tsayar da gudanar da taron a yau alhamis a bayan da sojojin kiyaye zaman lafiya na Faransa da na kasashen Afirka suka gana da 'yan tawaye domin shirya irin matakan tsaron da za a dauka.

Gwamnatin ta hadin kan kasa tana kokarin maido da harkokin yau da kullum tare da kayayyakin bukatu ga jama'ar kasar a bayan wata da watannin da aka yi ana gwabza yakin basasa.

XS
SM
MD
LG