Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Kashe Mutane Fiye Da 770 A Aljeriya - 2003-05-22


Gidan telebijin na Aljeriya ya ce mutane fiye da 770 sun mutu, yayin da wasu kusan dubu biyar suka ji rauni a girgizar kasa mafi muni da kasar ta gani cikin shekaru masu yawa.

A yau alhamis firayim ministan Aljeriya, Ahmed Ouyahia, yayi kashedin cewa adadin yawan mutanen da suka mutu zai karu a yayin da ma'aikatan agaji suke tono gine-ginen da suka rushe a wannan yanki mai tulin jama'a a bakin gabar tekun Bahar-Rum.

Kungiyar agaji ta Red cross ta kasa da kasa ta ce kungiyar Red Crescent ta Aljeriya tana aiki a wurin, inda take kokarin tono mutane ko gawarwakinsu daga karkashin gine-ginen da suka rushe. Faransa da Jamus ma sun tura ma'aikata da na'urorin bincike tare da karnuka masu iya sunsuno mutanen dake karkashin kasa.

Mutanen da suka ji rauni sun mamaye asibitocin yankin, yayin da wasu ke neman magani a wasu wuraren dabam. Jamia'an Aljeriya sun roki likitoci da ma'aikatan jinya da su taimaka, yayin da aka nemi jama'a su bada gudumawar jini.

An fi samun rahoton mutuwa a ciki da kuma kewayen biranen Roubia da Thenia, inda girgizar ta fi karfi, kimanin kilomita 60 a gabas da birnin Algiers.

A babban birnin kasar ma kanta, gine-gine da dama sun rushe, yayin da wutar lantarki ta dauke a wasu unguwanni. Mazauna birnin da dama da suka firgita, sun kwana a waje, yayin da aka yi ta samun motsin kasa.

Hukumar nazarin yanayin kasa ta Amurka ta ce wannan girgizar kasa ta jiya laraba da daddare ta kai karfin awu 6 da digo 7 a ma'aunin motsin kasa na Richter.

XS
SM
MD
LG