Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Ya Dage Takunkumin Tattalin Arzikin Da Aka Sanyawa Iraqi - 2003-05-22


Kwamitin Sulhun MDD mai wakilai 15 ya amince da kudurin da ya dage takunkumin tattalin arzikin da aka kafawa kasar Iraqi. Wakiliyar Muryar Amurka a majalisar ta ce kudurin ya kuma bai wa Amurka da Britaniya iko mai fadi kan harkokin tattalin arziki da na siyasar Iraqi, yayin da ya kebewa majalisar irin rawar da zata taka a kasar ta Iraqi.

Kwamitin Sulhun ya amince da wannan kuduri a bayan da aka yi kwana da kwanaki ana tattaunawa mai zafi, inda aka yi kwaskwarima sosai ga daftarin kudurin na farko domin yin la'akari da matsayin wasu manyan wakilan Kwamitin Sulhun.

Kudurin, wanda Amurka da Britaniya da Spain suka gabatar, ya kawo karshen mummunan takunkumin cinikayya da na kudin da majalisar ta kakabawa Iraqi a bayan da ta kai harin mamaye Kuwaiti a 1990, to amma kuma za a ci gaba da yin aiki da haramcin sayarwa da kasar makamai.

Syria, kasar Larabawa kwaya daya tak dake cikin Kwamitin Sulhun, ta kauracewa jefa kuri'ar. Syria ta ce tana bukatar karin lokaci domin nazarin wannan kuduri.

Duk da haka, jakadan Amurka a majalisar, John Negroponte, ya ce kwamitin sulhun ya hada kai domin kare muradun al'ummar Iraqi. Mr. Negroponte ya ce, "Dage takunkumin da aka yi wani muhimmin al'amari ne ga al'ummar Iraqi. Wani sabon babi ne da zai kyautata makomar al'ummar Iraqi da yankin baki daya."

A lokacin da ake tattaunawa kafin cimma kuduri na karshe, kasashen Faransa da Jamus da Rasha sun bayyana damuwa kan cewa daftarin farko ya bai wa Amurka da Britaniya iko maras iyaka kan albarkatun kasar Iraqi da harkokin siyasarta ba tare da ya bayyana wata rawar da MDD zata dauka ba im bayan aikin agajin jinkai.

Amma kuma wakilan Kwamitin sulhun sun cimma daidaiton ra'ayi a kan wasu matakan da zasu inganta nuna gaskiya da adalci wajen yin amfani da arzikin mai na Iraqi. Jakadan Faransa a MDD, Jean-Marc de la Sabliere, ya fada cewar kudurin alama ce ta samun ci gaba wajen zayyana matsayin MDD da kuma hakkin dake kan kasashen mamaya (AMurka da Britaniya) na mutunta dokokin kasa da kasa. Ya ce, "kudurin da muka zartas ba wai shine mafi dacewa ba. Amma an shigar da gyara a duk lokacin da aka tattauna a kai. Mun yi imani da cewa kudurin na yanzu ya samar da wani ginshikin da kasashen duniya zasu iya yin amfani da shi wajen tallafawa al'ummar Iraqi. Dalili ke nan da ya sa muka goyi bayan zartas da shi...."

Su ma Jamus da Rasha sun bayyana gamsuwarsu da wannan kudurin da suka ce na sassauci ne.

Kudurin ya tanadi cewa ikon da kasashen mamaya suke da shi na mulkin Iraqi zai kare da zarar an kafa gwamnatin da kasashen duniya suka yi na’am da ita a Iraqi. Wani sassaucin da masu gabatar da kudurin suka yi kuma shine na kyale kwamitin sulhun MDD ya sake nazarin wannan takunkumi cikin shekara guda. Kudurin ya bai wa wakilin MDD na musamman mai zaman kansa ikon taka rawa kafa gwamnatin rikon kwarya a Iraqi.

XS
SM
MD
LG