Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Shiga Tsakani A Rikicin Sudan Zai Gabatar Da Shirin Zaman Lafiya Na Karshe A Mako Mai Zuwa - 2003-05-22


Mai shiga tsakani a tattaunawar kawo karshen yakin basasar shekaru 20 a kasar Sudan, ya ce yana zana yarjejeniyar cimma zaman lafiya ta karshe da zai gabatarwa da sassan biyu a cikin mako mai zuwa.

Wakiliyar Muryar Amurka a gabashin Afirka, ta aiko da rahoton cewar daya daga cikin batutuwa masu sarkakiya da ake fuskanta shine na yadda za a yi da rundunonin sojan bangarorin biyu.

Mai shiga tsakanin dan kasar Kenya, Janar Lazaro Sumbeiywo, ya ce zai yi tattaki zuwa Sudan a mako mai zuwa domin ya gabatarwa da sassan biyu wannan shiri nasa na zaman lafiya. Janar Sumbeiywo ya ce, " Ina aikin rubuta kammalalliyar yarjejeniyar zaman lafiya. Na bullo da wata sabuwar dabara ta tinkarar wannan lamari a bayan da na tattauna da bangarorin biyu, kuma dukkansu sun yarda cewa wannan ita ce hanya mafi dacewa ta tinkarar lamarin. Zan tuntubi jami’an sassan biyu. Zan harhada bayanan da na ji daga sassan biyu in mika shi gare su...."

Sabuwar shawarar da Janar Sumbeiywo zai gabatar kokari ne na farfado da shirin samar da zaman lafiyar. A jiya laraba, an kammala zagaye na biyar na tattaunawa tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyar 'yan tawayen SPLA ba tare da sassan biyu sun cimma yarda a kan wasu muhimman batutuwa ba.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da ake ci gaba da yin mukabala a kai, shine yadda za a yi da rundunonin sojan gwamnati da na 'yan tawaye da zarar an rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya. A watan Yulin bara, gwamnatin Sudan da kungiyar 'yan tawayen SPLA sun yarda kan cewa za a kebe shekaru shida na wucin gadi wanda a lokacin za a tsame yankin kudancin kasar daga yin aiki da dokokin Shari'ar Musulunci. A cikin wannan lokaci, yankunan arewaci da kudancin Sudan zasu ga ko zasu iya yin zaman lafiya da junansu.

Arewacin Sudan dai yankin Musulmi ne yayin da a kudu yawancin jama'a ko dai Kiristoci ne ko kuma mutane masu yin addinan gargajiya.

A bayan cikar shekaru shida na wucin gadi, za a gudanar da kuri'ar raba-gardama, wadda zata bai wa yankin kudancin Sudan zabin ci gaba da zama cikin hadaddiyar Sudan, ko kuma zamowa 'yantacciyar kasa. Gwamnati tana so a hade rundunonin sojan sassan biyu a wannan lokaci da ake zaman wucin gadi.

Mohammed Dirdeiry na ofishin jakadancin Sudan a Nairobi yayi bayanin wannan matsayi, yana mai cewa, "Daya daga cikin ginshikan tabbatar da hadin kai, musamman a nan Afirka, shine samar da rundunar soja guda mai shugabanni guda a kasa guda. Idan har kungiyar SPLA tana yi da gaske ne, cewar ya kamata a samu hadin kai lokacin da ake zaman wucin gadi, to muna jin cewa ya kamata su amince da bukatar dake akwai ta samun rundunar soja guda daya a cikin kasar. Kasancewar rundunoni biyu, tamkar masifa ce. Idan har akwai wani abinda ya dame su a game da batun kafa rundunar soja guda kawai a kasa, to a shgirye muke mu dauki matakan ba su garanti, ko mu share musu hawaye. Amma ba zamu iya amincewa da rundunonin soja guda biyu a cikin kasa ba."

Amma kuma kungiyar SPLA ba ta yarda da hade sojojinta da na gwamnati a karkashin runduna guda ba, har sai bayan an gudanar da kuri'ar raba-gardama. Kakakin 'yan tawayen a birnin Nairobi, George Garang, ya ce ba zai yiwu kungiyarsu ta shiga cikin rundunar sojan da suke dauka a zaman ta Musulunci ba, wadda ke cike da mutane masu biyayya ga jam'iyyar National Islamic Front mai mulkin kasar.

Duk da bambancin ra'ayin dake tsakaninsu, malam Mohammed Dirdeiry na ofishin jakadancin Sudan a Nairobi yace yana da kwarin guiwar cewa za a iya samo hanyar warware wannan cijewa.

A shekarar 1983 kungiyar 'yan tawayen SPLA ta rungumi makamai ta fara yakar hukumomin birnin Khartoum, tana mai neman da a bai wa al'ummar kudancin kasar karin cin gashin kai. Mutane miliyan biyu suka mutu a wannan rikici, mafi yawansu a sanadin yunwar da yakin ya haddasa ba wai a bakin daga ba.

XS
SM
MD
LG