Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Mutane Fiye Da Dubu daya Da Dari Hudu Aka Ce Sun Mutu A Girgizar Kasar Aljeriya - 2003-05-23


Yawan mutanen da suka mutu a girgizar kasa mai muni da ta abku a Aljeriya ya haura zuwa dubu daya da dari hudu, yayin da wasu mutanen dubu bakwai da dari biyu suka ji rauni.

Har yanzu kuma, ma'aikatan agaji suna zakulo wasu mutanen da ransu daga karkashin gine-ginen da suka rushe, yayin da jami'ai suka ce har yanzu akwai wasu mutanen da ransu karkashin wadannan gine-gine.

Shugaba Abdoul-Azeez Bouteflika ya ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku, kama daga yau Jumma'a.

Ma'aikatan agaji daga kasashen duniya dabam-dabam, ciki har da Faransa, da Jamus, da Switzerland, da Rasha, da Italiya, da Morocco da kuma Spain suna tallafawa kokarin da ake yi na ceto mutanen da har yanzu ke da rai. Jami'an lafiya suka ce yawan wadanda suka ji rauni ya buwayi asibitocin yankin.

A dare na biyu a jere, 'yan Aljeriya masu yawan gaske sun kwana a waje, bisa fargabar cewa girgizar da kasa ke ci gaba da yi zata rushe sauran gine-ginen da suka lalace a sanadin babbar girgiza ta farko.

Girgizar kasa mai karfin awu 6 da digo 8 a ma'aunin motsin kasa na Richter ta abku ranar Laraba da daddare a kusa da gabar tekun Bahar Rum, a gabas da Algiers, babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG