Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rushe Rundunar Sojojin Kasar Iraqi - 2003-05-23


Kantoman da Amurka ta nada a Iraqi ya rushe rundunar sojoji da wasu cibiyoyi da dama na kasar da aka ce sune ginshikan tsohuwar gwamnatin Malam Saddam Hussein.

Wata sanarwar da Mr. Paul Bremer ya bayar yau Jumma'a a birnin Bagadaza, ta ce nan bada jimawa ba za a kirkiro da wata sabuwar rundunar soja ta Iraqi.

Har ila yau, wannan umurni nasa ya rushe ma'aikatun tsaro da yada labarai tare da wasu hukumomin tsaro dama ciki har da rundunar zaratan sojojin nan ta Republican Guard. Wannan hukumci na kantoman da Amurka ta nada ya shafi daruruwan dubban sojoji da ma'aikatan gwamnatin Iraqi wadanda a yanzu suka zamo marasa aikin yi.

Rundunar sojojin Iraqi dai ta wargaje tun watan jiya a lokacin da sojoji karkashin jagorancin Amurka suka hambarar da gwamnatin Saddam Husseini.

XS
SM
MD
LG