Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Dauke Da Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Spain Ya Fadi A Kasar Turkiyya - 2003-05-26


Wani jirgin sama dauke da sojojin kasar Spain dake kan hanyar zuwa gida daga ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar Afghanistan ya fadi a kusa da birnin Trabzon dake bakin tekun Bahar-ul-Aswad a kasar Turkiyya.

Dukkan mutane 74 dake cikin wannan jirgi sun mutu.

Wannan jirgi da ya taso daga garin Bishkek a kasar Kyrgyzstan a kan hanyar zuwa Zaragoza a kasar Spain, ya fadi cikin hazo mai yawa yau litinin da safe, a lokacin da yake kokarin sauka domin shan mai a filin jirgin saman Trabzon.

An ambaci jami'an Turkiyya suna fadin cewa matukin wannan jirgi na kasar Ukraine, ya bada rahoton cewa ba ya iya ganin hanyar saukar jirgin.

Ma'aikatar tsaron Spain ta tabbatar da cewa sojojinta 62 sun mutu a cikin wannan jirgi. Haka su ma ma'aikata 12 na wannan jirgi duk sun mutu.

XS
SM
MD
LG