Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yi Rashin Mohammed Yelwa Garvey - 2003-05-26


Allah Yayi rasuwa ma wakilin Muryar Amurka a Bauchi, Mohammed Yelwa Garvey.

Mohammed Yelwa Garvey ya rasu lahadi 25 ga watan Mayu a gidansa dake Unguwar Makama a Bauchi.

Marigayi Mohammed Yelwa Garvey, wanda ya rasu yana da shekaru kimanin 54 a duniya, sanannen dan jarida ne a kasar Hausa. Kafin ya fara aiki da Muryar Amurka, yayi shekaru kimanin 20 yana aiki tare da gidan Rediyon Nijeriya Kaduna, a matsayin wakili a wurare kamar Bauchi, Yola, Port Harcourt, Abuja da sauransu.

A saboda irin kwarewarsa wajen aikin jarida ne ma ya sa Sashen Hausa na Muryar Amurka ya roke shi da ya zamo mana wakili a yankin Niger Delta. Daga baya, saboda rashin lafiya, sai aka maida shi Bauchi kusa da 'yan'uwa da iyalinsa.

Mohammed Yelwa Garvey mutumin kasar Misau ne a Jihar Bauchi.

Dukkanmu a nan Sashen Hausa da kuma dukkan masu sauraronmu zamu yi kewarsa. Muna masu mika ta'aziyyarmu ga iyalan Mohammed Yelwa Garvey da dukkan 'yan'uwa da abokan arziki da kuma masu sauraronmu. Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, amin summa amin.

XS
SM
MD
LG