Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijeriya Sun Hana 'Yan Adawa Yin Zanga-Zanga - 2003-05-26


Hukumomin Nijeriya sun ki yarda su bada izni ga masu adawar dake son yin zanga-zangar rashin yarda da rantsar da shugaba Olusegun Obasanjo da ake shirin yi ranar alhamis.

Tuni har 'yan sandan sun rufe wani wurin da aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a birnin Kano dake arewacin Nijeriya. Babban mai adawa da gwamnatin Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana da karfi da tasiri a nan Kanon dabo.

Tarayyar Jam'iyyun adawa a Nijeriya ta kalubalanci gagarumar nasarar da aka ce shugaba Obasanjo ya samu a zaben ranar 19 ga watan Afrilu. A lokacin wannan zaben ne aka ce shugaba Obasanjo ya sake lashe kujerar shugabancin Nijeriya a karo na biyu a wannan zaben farko da fararen hula suka shirya cikin shekaru 20.

Muhammadu Buhari yayi zargin cewa magudi kawai aka tabka a wannan zabe, ya kuma yi kira ga shugaban da ya sauka a sake gudanar da zabe tsakani da Allah.

'Yan kallon zabe na kasashen duniya dabam-dabam ma sun soki yadda aka gudanar da zabubbukan na Nijeriya, suna masu fadin cewa a zahiri an tabka magudi mai yawan gaske a wurare da dama lokacin zaben.

XS
SM
MD
LG