Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hu Jintao Da Vladimir Putin Sun Gana Da Birnin Moscow - 2003-05-26


Shugaba Hu Jintao ya fara ziyarar aikinsa ta farko a wata kasar waje tun zamowa shugaban China, inda zai halarci liyafar cin abincin dare da shugaba Vladimir Putin na Rasha a Novo-Ogaryovo, wani gidan hutun shugaba dake karkara a kusa da Moscow.

A wajen wani taron 'yan jarida na hadin guiwa, Mr. Hu ya ce ya zabi kai ziyarar aikinsa ta farko zuwa Moscow ne domin nuna irin muhimmancin da China ta dora kan habaka dangantakarta da Rasha.

A bayan ganawarsu ta yau litinin, gobe sassan biyu zasu dukufa ga tattaunawa ka'in da na'in a fadar Kremlin. Ana sa ran mutanen biyu zasu takali batutuwa da dama, ciki har da ciniki da hadin kan tattalin arziki, da yaduwar cutar SARS da kuma wani aiki na shimfida bututun mai daga Angarsk dake gabashin yankin Siberiya a Rasha zuwa birnin Daqing na China.

Ziyarar mako guda da Mr. Hu zai yi a kasar Rasha, zata hada har da ziyartar birnin Saint Petersburg domin bukukuwan da za a yi na cikar shekaru 300 da kafa wannan birni.

XS
SM
MD
LG