Masu sauraronmu da jama'a daga wurare dabam-dabam suna ci gaba da aiko da sakonnin ta'aziyyar rashin da muka yi na wakilinmu a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, Mohammed Yelwa Garvey.
Daga Kontagora, mai sauraronmu Sani Buhari, ya aiko da wannan sako ta Email: "Ina mika gaisuwar ta'aziyar rashin da mu,da ku, da kuma Iyalan Marigayi Muhammed Yalwa Gavey suka yi. Allah ya jikan Sa amin."
Murtala Ahmed Birnin Magaji, shi kuma ya aiko mana da wannan sakon ta'aziyyar ta Email: "Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! Inna Lillahi Wa inna Ilaihim Raji'un...Babban dalilin rubuto maku wanna wasika tawa shine domin inyi maku ta'aziyyar rasuwar Malam Muhammed Yalwagabe, wato mai aiko maku da rahotanni. Allah na cewa acikin Qur'ani mai girma 'kulli nafsin za'ikatul mautu, wato kowace rai zata dandani mutuwa. To Allah ubangiji ya jikan muhammed Yalwagabe Ya gafarta masa, Ya kuma saka masa da aljannar firdausi, iyalinsa kuma Allah ubangiji ya kara masu hakurin jure rashin da muka yi...."
Shi ma abokin aikinmu na Sashen Hausa, na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Sani Adamu Bello, wanda ya san Mohammed Yelwa Garvey sosai, ya rubuto sakon ta'aziyya, yana fadin cewa, "Ina mai sanar da ku cewar,samun labarin rasuwar Muhammad Yalwa Gabi, Wakilunku a Shiyyar Arewa Maso Gabashin Nijeriya, da nayi ta Gidan Rediyonku yau Litinin da Yammacin agogon Tehran, ya kada min hanta sosai tare da jimanin wannan babban rashi da muka yi. A zahirin gaskiya na rasa yadda zan faro lamarin saboda farin sanin da na yi wa Alh. Yalwa Gabi. Babban addu'ata, Allah Ya jikansa Ya kuma gafarta masa. Dangane da haka, ina mai isar da sakon ta'aziyyata ga daukacin ma'aikatan Sashen Hausa na Muryar Amurka. Allah ya jikan Muhammad Yalwa Gabi, ya sanya Aljanna ta zama makomarsa. Iyalensa da ku abokan aikinsa, Allah Ya kara ba ku karfin hali da zuciyar jure wannan babban rashin da muka yi. Daga karshe, a madadin Ma'aikatan Sashen Hausa, na Muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ina mai kara mikon sakon ta'aziyyarmu gare ku. Allah Ya jikansa da Rahama tare da yafe masa kura-kuransa, mu kuma idan tamu ta zo mu sami cikawa da imani."
Mai sauraronmu Barrister Danlami Alhaji Wushishi, ya rubuto sakon ta'aziyya shi ma, yana fadin cewa, "Na samu labarin rasuwar Mohammed Yelwa gabi. ALLAH yajikan shi amin suman amin. YA KUMA ba wanda suka rage juriyar rashin, da kuma cika wa da imani amin."