Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawar Nijeriya Sun Ce Zasu Yi Gagarumar Zanga-Zanga - 2003-05-27


'Yan adawar Nijeriya sun ce zasu gudanar da gagarumar zanga-zanga a kafin rantsar da shugaban kasar da za a yi jibi alhamis, duk da haramta wannan zanga-zanga da gwamnati ta yi.

Jami'an Tarayyar jam'iyyun Siyasar Nijeriya, CNPP, da babbar jam'iyyar adawa ta ANPP, sun ce an shirya gudanar da zanga-zanga cikin 'yan kwanakin nan, ciki har da guda a Kanon Dabo, birni na biyu wajen girma a kasar.

'Yan sanda sun yi barazanar murkushe duk wata zanga-zangar da za a yi dangane da zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 19 ga watan Afrilu.

Wani dan takara mai adawa ya shiga kotu yana kalubalantar rantsar da shugaba Obasanjo da ake shirin yi, bisa hujjar cewa wannan wa'adi nasa na biyu ya samu ne a zaben da aka yi magudinsa.

Hukumomin zaben Nijeriya sun ayyana shugaba Obasanjo a zaman wanda ya lashe zaben, a bayan da suka ce ya samu kashi 62 yayin da Muhammadu Buhari ya samu kashi 32 daga cikin 100.

Sai dai kuma kungiyoyin 'yan kallo na kasashen duniya sun ce an tabka mummunan magudi a lokacin wannan zabe.

XS
SM
MD
LG