Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Mutane 22 Sun kamu Da Cutar SARS A Asiya... - 2003-05-27


Hukumomi a nahiyar Asiya sun bada rahoton karin mutane 22 kawai da suka kamu da mummunar cutar nan ta SARS mai kama da cutar hakarkari, yayin da ake ganin alamun cewa rayuwa ta fara komawa kamar ta kullum a bayan makonnin da aka yi ana fama da ukubar wannan cuta.

A kasar China an samu rahoton karin mutane 9 da suka kamu da cutar, yayin da wasu hudu suka mutu a yau talata.

Yawan ababen hawa ya karu a titunan birnin Beijing a cikin 'yan kwanakin da suka shige, yayin da aka ga alamun dakilewar yaduwar wannan cuta ta SARS.

Kamfanin safarar jiragen saman kasar China, Air China, ya ce yawan fasinjojin da yake dauka ya fara karuwa.

Hong Kong ta bada rahoton karin mutane biyu da suka kamu da cutar, yayin da wasu biyu suka mutu. Taiwan ta ce karin mutane 11 sun kamu da cutar, yayin da hudu suka mutu.

Hukumomi sun roki mutane da su koma ga gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba.

XS
SM
MD
LG