Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Ta Ce Yaki Da Ta'addanci Ya Kasa Wanzar Da Tsaro A Duniya - 2003-05-28


Kungiyar kare hakkin bil adama ta "Amnesty International" ta ce yaki da ta'addancin da Amurka take yi wa jagoranci ya kara jefa duniya cikin hatsari, ya kuma haddasa kara keta hakkokin jama'a a fadin duniya.

A cikin rahotonta na shekara-shekara da ta gabatar yau laraba, kungiyar mai cibiya a London ta ce idan har ana yaki da ta'addanci ne domin kawar da hatsari a duniya, to wannan manufa ta ci tura.

Ta ce an yi barazana ga hakkin jama'a, an gurgunta dokoki na kasa da kasa, yayin da aka kare gwamnatoci daga amsa tambayoyi kan ayyukansu, duka da sunan yaki da ta'addanci.

Babbar sakatariya ta kungiyar, Irene Khan, ta shaidawa taron 'yan jarida a London cewa matakan da ba za a iya amincewa da su ba a ranar 10 ga watan Satumbar 2001, yanzu sun zamo tamkar karbabbu na yau da kullum.

Kungiyar ta tsame Amurka tayi mata tatas a game da tsare mutanen da ake jin cewa 'yan ta'adda ne ba tare da ta gurfanar da su a gaban shari'a ba. Ms. Khan ta ce Amurka ta rungumi wata sabuwar turba mai hadarin gaske ta zaben dokokin kasa da kasa da zata yi amfani da su tare da take sauran.

Har ila yau Amnesty ta ce a yayin da hankalin duniya ya koma kan abubuwan dake faruwa a Iraqi, ana can ana take hakkin jama'a ka'in da na'in a wurare da dama, ciki har da Ivory Coast, Colombia, Burundi, Chechnya da Nepal.

Kungiyar ta yaba da ci gaban da aka samu a fagen kare hakkin jama'a a 2002, ciki har da kafa Kotun Shari'ar manyan Laifuffuka ta Duniya.

Rahoton na Amnesty International ya auna kamun ludayin kare hakkin bil Adama a kasashe da yankuna 151 a cikin shekarar 2002.

XS
SM
MD
LG