An sake rantsar da shugaba Olusegun Obasanjo domin fara wa'adi na biyu na jagorancin Nijeriya.
Gwamnati ta dauki matakan tsaro masu tsaurin gaske domin wannan buki da aka yi yau Alhamis a Abuja, babban birnin kasar, inda aka girka 'yan sandan kwantar da tarzoma dauke da makamai a duk fadin birnin na Abuja, da hanyar filin jirgin sama da kuma a gine-gine masu muhimmanci.
Har ila yau gwamnatin ta ki yarda ta kyale 'yan adawa su gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin.
Babbar jam'iyyar adawa ta Nijeriya tana kalubalantar gagarumar nasarar da aka ce Mr. Obasanjo ya samu a zaben, tana mai zargin gwamnati da laifin tabka magudi mai yawa a zaben na watan Afrilu.
Su ma 'yan kallo na kasa da kasa sun ce an tabka magudi sosai a wasu sassan kasar.
Kwanaki kadan kafin arantsar da Obasanjo, dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa, Muhammadu Buhari, ya kai kara kotu ya a neman a dakatar da rantsar da Mr. Obasanjo. Amma kotun daukaka karar ta ki amincewa da wannan roko, tana mai ba da hujjar cewa dakatar da rantsar Mr. Obasanjo zata haifar da wani halin da kasar zata zauna ba ta da shugaba.
Shugaba Obasanjo zai fara gudanar da wa'adinsa na biyu na shekaru 4 a kan karagar mulki cikin matsaloli masu yawa dake addabar kasar. Daga cikinsu har da zarmiya da cin hancin da ya zamo ruwan dare a Nijeriya, ga kuma rikice-rikicen kabilanci da na addini dake addabar wasu sassan kasar.