Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Ganin Alamun Shawo Kan Yaduwar Cutar SARS A Asiya - 2003-05-29


Taiwan ta bada rahoton sabbin kamuwa da cutar nan ta SARS guda 50, kwana guda a bayan da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce wannan tsibiri tana samun nasarar yaki da cutar mai kama huhu tare da kisa.

Wannan ita ce karuwa mafi girma ta yawan masu kamuwa da cutar SARS a tsibirin cikin kwanaki 6, amma kuma gwamnati ta sake jaddada cewar cutar tana raguwa.

Jami'an lafiya suka ce adadin da aka bayar a yau alhamis, ya hada da wasu mutane 40 da a can baya aka yi fargabar cewa sun kamu da cutar, kuma bincike ya tabbatar da cewa hakan ne. Suka ce a zahiri mutane 10 ne kawai sabbin kamuwa da cutar ta SARS.

A cikin wata sanarwar da ta bayar jiya laraba, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce da alamun an fara dakile yaduwar cutar ta SARS a Taiwan, bayan da aka shafe kwanaki da dama ana samun rahoton sabbin kamuwar da ba su shige goma ba. A wasu yankunan na nahiyar Asiya ma, sabbin kamuwa da cutar ta SARS suna raguwa.

XS
SM
MD
LG