Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Yin Girgizar Kasa A Aljeriya - 2003-05-29


Wata sabuwar girgizar kasa mai karfi ta jijjiga yankin babban birnin kasar Aljeriya.

Jami'ai suka ce girgizar ta baya-bayan nan da ta biyo bayan mummunar girgizar da aka yi a makon jiya, ta faru kafin ketowar alfijirin yau alhamis, kuma karfinta ya kai awu 5 da digo 8 a ma'aunin motsin kasa na Richter.

Hukumomi sun ce mutane da dama sun ji rauni, amma kuma babu mai tsanani.

Girgizar ta asubahin yau ta kuma lalata wasu gine-gine, ta kuma fi karfi a gabas da birnin Algiers, inda aka shafe mako guda da wasu kwanaki kasa tana motsi.

A ranakun talata da jiya laraba ma, an yi girgizar kasa mai karfi kamar ta yau a yankin na birnin Algiers da safe, inda mutane suka ringa fitowa kan tituna a firgice.

Irin wannan motsi da kasa ta ci gaba da yi a kai a kai, ya biyo bayan mummunar girgizar kasa mai karfin awu 6 da digo 8 a ma'aunin Richter, wadda ta kashe mutane fiye da dubu 2 da 200, yayin da wasu daruruwa suka bace ba a san inda suke har yanzu ba.

XS
SM
MD
LG