Shugabannin Isra'ila da na Falasdinawa suna ganawa a yanzu haka domin tattauna kokarin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya kafin taron kolin da zasu yi cikin mako mai zuwa da shugaba Bush na Amurka a kasar Jordan.
Ana sa ran cewa firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila da takwaransa na Falasdinu, Mahmud Abbas, zasu tattauna wani shirin tsagaita wuta, wanda a karkashinsa Isra'ila zata janye sojojinta daga wasu yankunan Falasdinawa, yayin da za a ba ta tabacin tsaro.
A yau alhamis an ambaci firayim ministan Falasdinu, Mahmud Abbas, yana fadin cewa yana sa ran kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas nan da mako mai zuwa.
Amma wani jami'in kungiyar ta Hamas ya ce har yanzu suna tattauna yadda zasu bulowa Isra'ila.