Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zafi Ya Kashe Mutane Kusan Dubu Daya A Indiya - 2003-06-02


Zafi mai tsanani da ake yi a kasar Indiya ya kashe mutane kuasan dubu daya a cikin makonni ukun da suka shige. Mutane 900 daga cikinsu, sun mutu ne a Jihar Andhra Pradesh na kudancin kasar.

Musulmi da Hindu suna ci gaba da addu'o'in neman ruwan sama a Hyderabad, babban birnin Jihar Andhra Pradesh, amma kuma masana yanayi sun ce za a ci gaba da wannan zafi mai tsanani har zuwa akalla 'yan kwanaki kadan dake tafe.

A jiya lahadi, zafin yayi kusan kaiwa awu 44 a ma'aunin zafi na Celsius. A wasu sassan jihar ta Andhra Pradesh, zafin ya kan kai awu 50 a ma'aunin an Celsius.

Har ila yau wannan zafi ya shafi kasar Bangladesh dake makwabtaka da wannan jiha ta Indiya. Jami'ai a Bangladesh sun ce mutane talatin suka mutu, yayin da wasu daruruwa suka kamu da laulayi na zafi a kasar.

Ana sa ran samun saukin wannan zafi nan gaba cikin wannan wata a lokacin da damina zata kama gadan-gadan a wannan yanki.

XS
SM
MD
LG