Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Gwabza Kazamin Fada Tsakanin Sojojin Gwamnati Da Na 'Yan Tawaye A Monrovia - 2003-06-09


An ci gaba da gwabza kazamin fada a rana ta hudu a jere a tsakanin 'yan tawayen Liberiya da sojoji masu yin biyayya ga shugaba Charles Taylor a kusa da Monrovia, babban birnin kasar. A wani gefe, an kaddamar da sabon yunkurin kawo karshen wannan fada.

An shirya Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, zai gana a yau litinin domin tattauna kazancewar fada cikin 'yan kwanakin nan a wajen Monrovia.

A halin da ake ciki, jami'an shiga tsakani na Afirka ta Yamma, suna kan hanyar zuwa birnin domin su yi kokarin shirya tsagaita wuta.

Sojojin Faransa sun yi amfani da jiragen helkwaftoci domin kwashe 'yan kasashen waje saboda wannan fada, yayin da dubban mazauna Monrovia sun gudu zuwa tsakiyar birnin, domin gujewa fadan da ake gwabzawa a unguwannin bayan gari.

Masu shiga tsakani na kasa da kasa sun bayar da sanarwar cewa tattaunawar neman zaman lafiyar da aka shirya gudanarwa yau litinin aGhana tsakanin gwamnatin Liberiya da wakilan 'yan tawaye, yanzu an dage sai ranar laraba.

Jiya lahadi, babbar kungiyar 'yan tawayen Liberiya mai suna L.U.R.D. (Liberians United for Reconciliation and Democracy), ta bukaci shugaba Charles Taylor da yayi murabus cikin kwanaki uku, ko kuma ya fuskanci wani sabon farmaki na neman kwace babban birnin.

A makon da ya shige, Kotun MDD mai bin kadin laifuffukan yaki a kasar Saliyo, ta tuhumi Mr. Taylor dangane da munanan ayyukan ta'asar da aka aikata a lokacin yakin basasar Saliyo. Jami'an MDD da na kasashen yammaci, suna zargin Mr. taylor da laifin tara dukiya ta hanyar hura wutar fitinu a yankin Afirka ta Yamma.

XS
SM
MD
LG