Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Ould Taya Na Mauritaniya Ya Ce Sojojinsa Sun Murkushe Yunkurin Juyin Mulki - 2003-06-09


Shugaba Maaouya Ould Taya na Mauritaniya, ya ce an murkushe wani yunkurin juyin mulki a yayin da sojojinsa suka sake kwato babban birnin kasar, Nouakchott, a bayan fadan kwana guda da rabi.

A cikin jawabin da yayi ta rediyo yau litinin, shugaban ya ce sojoji masu biyayya ga gwamnati sun murkushe abinda ya kira, "yunkurin kawo karshen gina kasa da ceton al'umma."

Shaidu sun ce a yanzu sojojin gwamnati ne suke rike da fadar shugaban kasa, da wasu muhimman cibiyoyi a tsakiyar birnin Nouakchott. Magoya bayan shugaban sun fantsama kan tituna domin murnar nasarar da sojoji masu biyayya ga gwamnati suka samu a wannan artabu.

Wannan murna ta su ta biyo bayan zaman tsananin rudani na tsawon sa'o'i 36, inda sau biyu cikin wannan lokaci gwamnati take ikirarin cewar ta murkushe wannan bore. An samu rahotannin dake cewa sojojin 'yan tawaye sun shiga cikin fadar shugaban kasar a jiya lahadi.

Har ila yau, an yi ta samun rahotannin da suka sha bambam kan inda shugaba Ould Taya yake. Amma kuma shaidu sun ce an kawo sojoji daga wasu sassan kasar ta Mauritaniya domin su kwantar da wutar wannan bore.

Wannan bore ya biyo bayan matakan da gwamnati ta dauka kwanakin baya na yin tarnaki wa masu kishin addini. Masu kishin addinin dai suna yin adawa da manufofin gwamnatin da suke gani na goyon bayan Amurka ne, da kuma huldar jakadancin da ta kulla da Isra'ila.

XS
SM
MD
LG