Shugaba Bush ya ce lokaci na zuwa da za a gano cewar Amurka ta yi daidai da ta hambarar da gwamnatin Saddam Hussein.
Shugaban ya bayyana wannan a lokacin da yake amsa tambayar da wani dan jarida yayi masa a yau litinin, kan ko rashin gano muggan makaman kare-dangi da Amurka ta yi ta shelar cewa Iraqi ta mallaka, ya raunana martabar Amurka.
Mr. Bush ya ce Iraqi tana da shiri na kera makamai, kuma rahotannin leken asirin da aka yi ta samu cikin shekaru goman da suka shige sun gaskata hakan.
Shugaba Bush bai fito ya ambaci makaman kansu ba. Amma a cikin hirarrakin da aka yi da su cikin 'yan kwanakin nan, jami'an gwamnatin ta Amurka sun ba da tabbacin cewa za a gano wadannan makamai.
Ikirarin cewar Iraqi ta mallaki wadannan makamai shine babban dalilin da aka bayar na farmakin sojan da Amurka ta jagoranci kaiwa a kan Iraqi.