Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahmud Abbas Yayi Tur Da Yunkurin Isra'ila Na Kashe Jigon Hamas - 2003-06-10


Firayim ministan Falasdinawa, Mahmud Abbas, ya bayyana yunkurin da Isra'ila ta yi na kashe wani jigon kungiyar Hamas a zaman ta'addanci da nufin gurgunta kokarin wanzar da zaman lafiya.

Mutumin da Isra'ila ta nemi kashewa, Abdel-Aziz Rantisi, wanda shine kakakin Hamas, ya lashi takobi daga kan gadonsa a asibiti cewar Hamas zata ci gaba da kai hari kan kasar ta Isra'ila.

Abdel-Aziz Rantisi ya ji rauni a lokacin da wani jirgin helkwafta na Isra'ila ya kai masa farmaki, inda wasu Falasdinawan su uku suka mutu, wasu akalla 20 suka ji rauni yau talata a birnin Gaza.

Shaidu sun ce jigon na kungiyar Hamas ya tsallake rijiya da baya, a lokacin da yayi tsalle ya fita daga cikin motarsa kafin wani makami mai linzami ya ragargaza motar ta koma garwa.

A furucin da yayi ga gidan telebijin na al-Jazeera, Malam Rantisi ya lashi takobin cewa Hamas zata dauko fansar wannan harin.

Malam Rantisi fitacce ne wajen sukar kokarin firayim ministan Falasdinawa Mahmud Abbas, na ganin an daina kai hare-hare kan Isra'ila.

XS
SM
MD
LG