Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Faransa Sun Isa Gabashin Kwango-Ta-Kinshasa - 2003-06-10


Ayarin farko na zaratan sojojin Faransa sun isa yankin gabashin kasar Kwango-ta-Kinshasa, a wani bangare na rundunar gaggawa ta kasa da kasa da zata yi kokarin kashe wutar fadan kabilancin da ake gwabzawa a yankin.

Sojojin Faransa su kimanin 40 sun sauka a garin Bunia a cikin wani jirgin saman soja, a matakin farko na girka sojoji kimanin dubu 1 da 400 na wannan runduna.

Nan gaba a yau talata ake sa ran karin sojoji 100 zasu isa can.

An tura wadannan sojoji ne domin su agazawa wata rundunar sojan majalisar Dinkin Duniya karama wadda ta kasa tabuka komai wajen kawo karshen fadan kabilancin da aka yi wata guda ana gwabzawa, inda aka kashe daruruwan mutane, yayin da wasu dubbai suka rasa matsuguni.

XS
SM
MD
LG