An tura sojojin gwamnatin kasar Peru domin su yi kokarin ceto mutane 60 wadanda wasu mutanen da ake kyautata zaton 'yan tawaye masu ra'ayin gurguzu ne suka sace jiya litinin daga wani sansanin ma'aikatan shimfida bututun mai a can cikin tsaunukan Andes.
Jami'ai suka ce an sace mutanen ne a lokacin da wasu mutane fiye da 100 dauke da makamai suka kai farmaki kan wannan sansani wanda kamfanin man fetur na kasar Argentina mai suna TECHINT ke gudanarwa.
Wata sanarwar da gwamnatin kasar Peru ta bayar jiya litinin da maraice, ta ce hukumomi sun dauki matakan da suka kamata domin tabbatar da kwato mutanen da aka sace din.
Jami'ai suka ce wadanda suka sace wadannan mutane sun bukaci da a biya su fansar dala miliyan daya kafin su sako su.
'Yan sanda sun yi imanin cewa 'yan tawayen "Shining Path" masu ra'ayin gurguzu irin na Mao Tse Tung sune suka sace mutanen.