Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Yi WA Sojojin Amurka Kwanton-Bauna Yayin Da Suke Farautar Masu Biyayya Ga Saddam Hussein - 2003-06-16


Sojojin Amurka dake Iraqi sun bayar da rahoton cewa an kai musu karin hari na kwanton-bauna a yayin da suke farautar masu biyayya ga tsohuwar gwamnatin kasar a garuruwa da kauyukan dake kusa da birnin Bagadaza.

Hedkwatar rundunar sojohjin Amurka ta ce maharan sun harba gurneti da bvindigar roka a kan wata kwambar sojojin Amurka jiya lahadi a kusa da al-Mushahidah, a arewa da birnin Bagadaza. Amma kuma wannan gurneti ya fada kan wata motar safa ta farar hula dake kokarin wuce sojojin na Amurka a lokacin.

Hedkwatar ta rundunar sojojin Amurka ta ce ba a san yawan mutanen ad suka mutu a motar safar ba. Wani kakakin Amurka a Bagadaza ya ce sojojin Amurka da dama sun ji rauni a wannan harin, da kuma wani shi ma na gurneti da aka kai kan wata kwambar soja a kusa da ad-Dujayl a arewa da Bagadaza.

Sojojin Amurka sun shiga rana ta biyu ta farautar magoya bayan jam'iyyar Baath, wadanda suka kai munanan hare-hare kan sojojin Amurka tun daga farkon watan Mayu.

XS
SM
MD
LG