Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Dubu 400 Sun Rasa Gidajensu A Dalilin Ambaliyar Ruwa A Indiya - 2003-06-16


Jami'an Indiya sun ce ambaliyar ruwa da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake juyewa sun sanya daruruwan dubban mutane sun rasa gidajensu a Jihar Assam dake arewa maso gabashin kasar.

Jami'an Jihar ta Assam sun ce ambaliyar ruwan ta raba mutane dubu 400 da gidajensu a kauyuka 450. Suka ce ruwan ambaliyar ya bata ruwan sha, inda mutane masu yawan gaske a yanzu suke fama da mummunan karancin ruwan sha.

A yanzu, gwamnatin jihar ta damu kan cewa ruwan sama mai yawan gaske dake sauka zai sa babban kogin dake Jihar ya cika ya batse, har ma ya malale yankin dake kusa da Guwahati, babban birnin Jihar.

Gwamnatin jihar ta Assam ta ce irin wannan ambaliya zata iya malale babban filin jirgin sama dake wannan birni.

XS
SM
MD
LG