Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsoffin 'Yan Majalisar Zartaswar Britaniya Sun Ce Tony Blair Yayi Karin Gishiri Kan Barazanar Da Wai Iraqi Take Yi Musu - 2003-06-17


Wasu tsoffin 'yan majalisar zartaswar Britaniya, sun zargi gwamnati da laifin yin amfani ta hanyar da ba ta dace ba da bayanan leken asiri marasa tushe domin gabatar da hujjar kai wa kasar Iraqi farmakin soja.

Tsohon sakataren harkokin wajen Britaniya, Robin Cook, ya shaidawa wani kwamitin majalisar dokoki cewar gwamnatin Firayim Minista Tony Blair ta yi karin gishiri kan barazanar Iraqi da makamanta na kare-dangi.

Ita ma tsohuwar sakatariyar raya kasashen ketare ta Britaniya, Clare Short, ta ce ta yi imani Firayim minista yana da laifin abinda ta kira "yaudara cikin aminci" a shirye-shiryen kai farmakin soja kan Iraqi.

Firayim ministan na Britaniya ya musanta cewa ya yaudari al'ummar kasar.

Tsoffin ministocin a gwamnatin Britaniya suna magana ne a wajen zaman fara gudanar da bincike a majalisar dokoki kan yadda gwamnatin ta kasar ta yi amfani da bayanan leken asiri kan kasar Iraqi.

XS
SM
MD
LG