Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Karfafa Guiwar Zanga-Zangar Da Ake Yi A Iran In Ji Colin Powell - 2003-06-17


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce Amurka tana karfafa guiwar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da ake yi a Iran, amma kuma ya musanta zargin da hukumomi a birnin Teheran suka yi cewa Amurka ce ta kitsa wannan tashin hankali.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida a cikin jirgin sama kan hanyarsa ta zuwa Cambodia, Mr. Powell ya ce ya kamata a kyale 'yan Iran su yi zanga-zanga cikin lumana a saboda hakkin da suke da shi na ganin kyautatuwar rayuwarsu.

Amma kuma ya ce Amurka ba ta hura wutar wannan fitina, har ma ya ce watakila gwamnatin Iran tana kokari ne ta tura ma wasu matsalolin dake addabarta.

Dalibai a birnin Teheran sun yi kwanaki bakwai a jere suna yin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a cikin dare. An ce an samu tashin hankali a wasu biranen lardunan kasar.

XS
SM
MD
LG