Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kan Sojojin Amurka A Iraqi, Aka Kashe Guda, Aka Raunata Biyu - 2003-06-19


Rundunar sojojin Amurka ta ce an kai hari kan sojojin taron dangi a kudu da birnin Bagadaza, inda aka kashe sojan Amurka daya, aka raunata wasu akalla biyu.

An kai wannan harin yau alhamis a bayan garin Bagadaza. Gurnetin da ake harbawa da bindigar roka ta fada kan wata motar daukar marasa lafiya ta sojojin Amurka, motar ta kama da wuta.

Wannan harin an yau alhamis ya faru a unguwar da aka kashe wani sojan Amurka daya aka raunata wani guda jiya laraba a wani gidan mai da sojojin suke gadi.

Jami'an Amurka suna dora laifin hare-haren da ake yawaita kaiwa sojojin taron dangi cikin 'yan kwanakin nan a kan wadanda har yanzu suke yin biyayya ga hambararren shugaban Iraqi, Saddam Hussein. A cikin 'yan kwanakin nan kuma, sojojin taron dangi sun kai sumame da yawa domin murkushe sauran masu yin adawa da su.

A jiya laraba, an kashe dan Iraqi guda aka raunata wasu 12 a lokacin da kwanson nakiya ya fada kan wani ofishin 'yan taron dangi a birnin Samarra, dake arewa da Bagadaza. Babu wani sojan Amurka da ya ji rauni, kuma ana ci gaba da bincike.

A wani labarin kuma, babban jami'in man fetur na Iraqi, Mohammed al-Jibouri, ya ce a ranar lahadi mai zuwa Iraqi zata koma ga sayar da manta a kasashen ketare, bayan dakatar da yin hakan da aka yi na watanni uku.

XS
SM
MD
LG