Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fasa Bututun Man Fetur Na Biyu A Kasar Iraqi - 2003-06-23


Wani jami'in man fetur na Iraqi ya ce wata fashewar da ta abku kusa da bakin iyakarsu da kasar Sham ko Syria, ta lalata wani bututun na jigilar man Iraqi.

Jami'in bai bayar da cikakken bayani wannan fashewar ba, wadda ita ce ta biyu tun shekaranjiya asabar, sannan kuma har yanzu jami'an Amurka ba su tabbatar da labarin ba.

Hukumomin Amurka suna binciken musabbabin fashewar ta asabar, wadda ta gurgunta wani muhimmin bututun mai dake yamma da birnin Bagadaza.

A can wani gefen kuwa, Amurkawa masu mulkin Iraqi sun ce a mako mai zuwa zasu fara daukar wadanda zasu yi aiki a sabuwar rundunar sojojin Iraqi wadda zata maye gurbin ta Saddam Hussein da aka rushe. Mashawarci ba'Amurke, Walter Slocomb, ya ce rundunar farko ta sojoji dubu 12 zata fara aiki a shekara mai zuwa, yayin da a cikin shekaru uku rundunar zata habaka ta kunshi sojoji dubu 40.

A halin da ake ciki dai, jami'an Amurka suna binciken ko hambararren shugaban Iraqi Saddam Hussein, ko kuma 'ya'yansa maza suna cikin wata karamar kwambar motocin da aka lalata da makami mai linzami a makon da ya shige a kusa da bakin iyaka da Syria.

Manyan jaridun Amurka suka ce masana suna gwajin kwayayen halittar mutanen dake cikin kwambar motocin domin gano ko su wanene. Ana nazarin gawarwaki da gabobin mutanen da aka samu daga wurin da aka kai wa harin ranar laraba, amma jaridun sun ambaci jami'an Amurka suna fadin cewa har yanzu babu shaidar cewa Saddam ko 'ya'yansa Uday da Qusay suna cikin kwambar.

XS
SM
MD
LG