Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Britaniya Shida, Aka Raunata 8 A Iraqi - 2003-06-25


Sojojin Britaniya a Iraqi suna farautar maharan da suka kashe dakarun Britaniya shida, suka raunata wasu guda takwas, a hare-hare biyu jiya talata a kudancin kasar.

Sakataren tsaron Britaniya, Geoff Hoon, ya ce sojoji shidan da aka kashe, kurfau ne masu horas da 'yan sandan Iraqi.

An ambaci shaidu suna fadin cewa an kashe sojojin na Britaniya ne a lokacin musanyar wuta da mutanen yankin, wadanda suka fusata da irin matakan da sojojin na Britaniya suka dauka a lokacin da suke farautar manyan makamai a yankin kwanakin baya.

Mazauna yankin sun kuma ce an kashe 'yan Iraqi hudu aka raunata wasu guda 17 a lokacin wannan dauki-ba-dadi.

XS
SM
MD
LG