Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Liberiya Sun Shiga Cikin Birnin Monrovia - 2003-06-25


'Yan tawayen Liberiya, wadanda suka kutsa kai cikin Monrovia, babban birnin kasar, sun ce ba zasu daina fada ba, har sai sun kwace wannan birni.

wannan sanarwa ta yau laraba, ta zo a daidai lokacin da 'yan tawayen suke dauki-ba-dadi da sojoji masu biyayya ga shugaba Charles Taylor a yankin tashar jiragen ruwa dake unguwannin yammacin birnin, kilomita 5 kacal daga fadar Mr. Taylor.

Shaidu sun ce kwanson nakiya na fashewa a unguwanni da dama na birnin, abinda ya sa mazauna wannan birni suke arcewa, ko kuma kulle kansu a cikin gidajensu.

A cikin jawabin da yayi a rediyo, Mr. Taylor ya bayyana wannan farmaki na 'yan tawayen a zaman ta'addanci, ya kuma ce sojojinsa zasu gwabza da su har sai karfinsu ya kare. Ya musanta rahoton cewa ya gudu daga birnin, yana mai fadawa jama'a cewa rayuwarsa ba ta fi tasu muhimmanci ba.

A jiya talata 'yan tawaye suka kaddamar da farmakinsu na baya bayan nan. Dakaru masu biyayya ga gwamnati da na kungiyar 'yan tawayen "LURD" suna zargin juna da laifin sake tayar da fada.

Wannan fada shi ya kawo karshen shirin tsagaita wutar da aka rattaba wa hannu a makon da ya shige a kasar Ghana.

XS
SM
MD
LG