Kungiyoyin kishin Falasdinu sun lashi takobin daukar fansar hare-haren da suka kashe Falasdinawa hudu a yau laraba, abinda ya kawo tababar yiwuwar kulla shirin tsagaita wuta da Isra'ila.
Bangaren soja na kungiyar Hamas ya ce zai dauki fansa kan Isra'ila a saboda hare-haren da suka kashe membobinta biyu yau laraba a yankin Beit Hanoun na zirin Gaza.
haka kuma a yau laraba manyan shugabannin kungiyoyin kishin Falasdinu suka musanta rahotannin cewa sun yarda da tsagaita wuta na wucin gadi, suna masu fadin cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.
A wani gefen kuwa, Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a zirin Gaza ta kashe wasu Falasdinawan biyu ta raunata 14. Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan 'yan Hamas wadanda, a cewarta, suna shirin kai farmaki kan wata unguwar share ka zauna ta yahudawa a zirin Gaza.