Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Hukumar Leken Asiri A Amurka Ta  Ce babu Tabbas Cewar Motocin Da Aka Gano A Iraqi Na Kera Makamai Masu Guba Ne - 2003-06-26


Wata jarida a nan Amurka ta bayar da rahoton cewa daya daga cikin hukumomin leken asirin Amurka, ta musanta ikirarin da hukumar leken asiri ta C.I.A. ta yi, cewar wasu motocin tafi-da-gidanka da aka gano a Iraqi dakunan harhada makamai masu guba ne.

Jaridar New York Times ta ambaci jami'an Amurka suna fadin cewa Hukumar leken asiri ta ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta rubuta wani rahoto a farkon wannan watan, inda take cewa har yanzu babu wata kwakkwarar shaidar cewa wadannan motoci sun gaskata ikirarin cewa Iraqi tana kera makamai masu yada kwayoyin cuta.

Jaridar ta NYT ta ce wannan rahoto ya saba da wadanda hukumar leken asiri ta CIA da kuma hukumar leken asiri ta ma'aikatar tsaron Amurka suka bayar, inda suke cewa wadannan motoci masana'antu ne masu sauki da kuma tasiri na kera makamai masu yada cuta.

A watan da ya shige, a lokacin da yake magana a gidan telebijin na kasar Poland, shugaba Bush yayi magana kan gano wadannan motoci, inda har ya ce Amurka ta gano makaman kare dangin da take nema a Iraqi.

Amurka da Britaniya sun bayar da hujjar fuskantar barazana ta zahiri daga makaman nukiliya, da guba da kuma na cuta daga Iraqi a zaman dalilinsu na kai mata farmaki. Amma kuma, har yanzu sojojin Amurka dake kasar ba su samu wata shaidar cewa Iraqi tana da haramtattun makamai ba.

XS
SM
MD
LG