Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijeriya Ta Haramta Yajin Aikin Da Ake Shirin Yi - 2003-06-27


Gwamnatin Nijeriya ta ce yajin aiki na gama gari da ake shirin farawa a mako mai zuwa a saboda karin farashin man fetur, na haramun ne.

A cikin sanarwar da ta bayar alhamis, gwamnatin ta ce kungiyoyin kwadago ba su ba ta sanarwar kwanaki 15 da ake bukata kafin fara yajin aiki ba. Gwamnatin ta roki ma'aikata da kada su shiga cikin wannan yajin aiki.

Babbar kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC, ta ce zata fara yajin aikin har illa ma sha Allahu daga ranar litinin.

Kungiyoyin ma'aikatan kamfanonin jiragen sama sun bayyana goyon baya ga babbar kungiyar kwadagon, suna masu cewa daga ranar litinin za a rufe dukkan filayen jiragen sama na Nijeriya. Har ila yau, wata kungiyar rajin dimokuradiyya mai suna "United Action for Democracy" ita ma ta bayyana goyon bayanta ga wannan shirin yajin aiki.

Ma'aikata a Nijeriya sun fusata da shawarar da shugaba Olusegun Obasanjo ya yanke ta janye rangwamen farashin mai, matakin da ya kara farashin man da kashi hamsin daga cikin dari.

Gwamnati dai ta ce tana hasarar kudi kusan dala miliyan dubu biyu a kowace shekara a saboda rangwamen da take yi na farashin mai. Ta ce zai fi kyau a kashe wannan kudi mai yawa wajen ayyukan kyautata jin dadin rayuwar jama'a.

XS
SM
MD
LG