Shugabannin kungiyoyin kishin Falasdinu sun ce sun yarda zasu daina kai hare-hare a kan Isra'ila na tsawon watanni uku.
A yau Jumma'a aka samu tabbacin cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, a bayan da aka yi kwana da kwanaki ana san yin hakan. Amma kuma, jami'an dake cikin tattaunawar sun ce ba za a bayar da cikakkiyar sanarwa ba sai ranar lahadi.
Manyan kungiyoyin Falasdinawa uku, watau Hamas da Islamic Jihad da kuma al-Fatah ta Mallam Yasser Arafat, sune suka zana wannan yarjejeniya, wadda ta tanadi tsagaita wutar watanni uku, yayin da Isra'ila kuma zata kawo karshen hare-haren sojan da take kaiwa a kan Falasdinawa.
Har ila yau, gidan telebijin na Isra'ila ya bada rahoto a yau Jumma'a cewa an cimma yarjejeniya a tsakanin Isra'ila da Majalisar Mulkin Kai ta Falasdinawa, wadda a karkashinta Isra'ila zata janye sojojinta daga wasu sassan zirin Gaza da Yankin Yammacin Kogin Jordan, watakila ma nan da ranar litinin.
Har yanzu jami'an sassan biyu ba su tabbatar da gaskiyar labarin cimma yarjejeniyar ba.