Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda A Nijeriya Sun Yi Amfani Da Barkonon Tsohuwa Domin Tarwatsa Masu Zanga-Zanga - 2003-06-30


'Yan sanda a Nijeriya sun harba barkonon tsohuwa, da bindigogi a sama domin tarwatsa 'yan zanga-zanga, a yayin da aka fara gudanar da yajin aiki na gama gari kan karin farashin man fetur.

Shaidu sun ce jami'an tsaro sun gwabza da 'yan zanga-zanga a Abuja, babban birnin kasar, da kuma Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwancin Nijeriya, a bayan da ma'aikata suka yi ko oho da wani umurnin kotu da ya hana gudanar da zanga-zangar. Suka ce a wasu wurare, 'yan zanga-zanga sun kakkafa shingaye, suka kona tayu da wasu kayayyakin a kan hanyoyi.

Kantuna da ofisoshin da dama ba su bude ba a yau, wasu saboda fargabar 'yan kwasar ganima.

Kungiyoyin kwadago sun fusata da shawarar da shugaba Olusegun Obasanjo ya yanke ta janye rangwamen rfarashin mai. Wannan mataki ya kara farashin mai a kasar da kashi 54 daga cikin 100.

Shugaba Obasanjo dai ya ce ba zai janye wannan karin farashi ba, a saboda a cewarsa ana bukatar wannan kudi domin kula da lafiyar jama'a da kuma ilmi.

Mr. Obasanjo yayi kashedin cewa duk wani ma'aikacin da ya zauna a gida zai yi hasarar albashinsa na tsawon kwanakin da bai je aikin ba.

Ana fargabar cewa wannan yajin aiki yana iya rikidewa ya koma mummunar zanga-zanga ta nuna kin jinin Obasanjo a Nijeriya. Shugabannin hamayya na kasar sun zargi Cif Obasanjo da laifin tabka magudi a zaben watan Afrilu.

Koda yake Nijeriya ita ce kasa ta takwas a jerin masu arzikin man fetur a duniya, kasar tana fama da mummunan karancin tataccen mai. Akasarin man fetur da gas da ake sayarwa a kasar, ana sayowa ne daga kasashen waje.

XS
SM
MD
LG